IQNA

Gangamin Ranar Quds A Gaban Ofishin Jakadancin Isra’ila A Brussels

22:27 - June 22, 2017
Lambar Labari: 3481632
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gangami a gaban ofishin jakadancin Isra’aila a ranar Quds ta duniya a birnin Brussels na kasar Belgium.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wanann gangami za a gudanar da shi ne a karon farko a gaban ofishin jakadancin Isra’ila a birnin na Brussels a gobe Juma’a.

Masu gangamin dai za su daga tutocin palastine da kuma kwale da kyallayen da suke da rubuce-rubucen nuna goyon baya ga al’ummar Palastine, da kuma yin tir da Allah wadai da mamayar da Isra’ila take yi wa yankunansu, da kuma zaluntarsu tare da danne musu hakkoki, da keta alfarmar wurarensu an addini musamman masallacin Quds.

Wanann gangami dai zai hada lauyoyi da masu fafutuka gami da malaman jami’a da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma ‘yan jarida, gami da sauran mutaen gari masu adawa da zaluncin Isra’ila a kan Palastinawa.

3612248


captcha