IQNA

Musulmin Birnin Bolton Suna Taimaka ma Yara Marassa Karfi

18:58 - June 23, 2017
Lambar Labari: 3481636
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin msulunci mazauna birnin Bolton a kasar Birtaniya suna gudanar da wani aikin alkhairi na taimaka ma kananan yara marassa karfi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na thisislancashire cewa, wannan cibiya da ke gudanar da ayyukan alkhairi, tana karbar tallafi daga musulmi domin bayarwa ga yara marassa lafiya da marassa karfi.

Daga cikin kayan da suke saye kuwa har kayan wasa da kuma abubuwan ci da yara suke bukata, gami da daukar nauyin sayen magungunasu ga wadanda suke kwance a asibiti suna bukatar agaji.

Islam Atcha daya daga cikin mambobin wannan wannan cibiya ya bayyana cewa, babbar manufarsu ita ce kara samar da yanayi na fahimtar juna atsakanin musulmi da sauran mabiya addinai, kuma wannan aiki da suke yi musulnci ne ya koyar da su yin hakan.

Daga karshe ya yi fatan alkhairi ga dukaknin musulmi da kuma fatan za a yi salla lafiya.

3612357


captcha