IQNA

Iran Ta Yi Allah Wadai Kan Yunkurin Kai Harin Ta'addanci Kan Haramin Makkah

23:55 - June 24, 2017
Lambar Labari: 3481637
Bangaren kasa da kasa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tofin Allah tsine kan yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah tare da jaddada bukatar fadakar al'ummar yankin gabas ta tsakiya kan hatsarin ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi a yau Asabar ya yi tofin Allah tsine kan yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah tare da fayyace cewa: Wannan yunkuri yana nuni da cewa ne akidar ta'addanci wata babbarbarazana ce ga duniya musamman ga al'ummar musulmi da kasashensu, kuma yunkurin kai harin ta'addanci kan haramin Makkah lamari ne da ke fayyace cewa: Akidar ta'ddanci bata da alaka da addini, mazhaba , yanki ko al'umma.

Qasimi ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana Allah wadai da duk wani aikin ta'addanci a kowane sako na duniya kuma a shirye take ta gabatar da gudumawarta wajen murkushe 'yan ta'adda da ayyukan ta'addanci a duniya.

A jiya Juma'a ce wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin haramin Makkah bayan da jami'an tsaron Saudiyya suka masa kawanya bayan samun bayanan asiri kan mummunar aniyarsa ta kai harin wuce gona da iri kan al'ummar musulmi a karshen Juma'ar watan ramadana mai alfarma.

3612742


captcha