IQNA

Jagora Ya Yi Afuwa Ga Wasu Fursunoni Domin Idin Fetr

22:40 - June 25, 2017
Lambar Labari: 3481641
Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya amince da afwa ko kuma rage yawan sarkan da aka dorawa wasu fursinoni saboda zagayowar ranar sallah karama.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jagora ya bayar da bayanin cewa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei yana fadar haka a yau lahadi, ya kuma kara da cewa jagoran ya amince da yin afwa, ko rage dauri, ko kuma sauya hukunci ga fursinoni dubu da arbain da tara, wanda alkalin alkalan kasar ya gabatar masa.

Ayatollah Amuli Larijani alkalin alkalai na kasa shi ne ya isar da sakon neman hakan ga jagora, har'ila yau hukumar bada horo da kuma ta kotun soje duk sun amince da afwan da alkalin alkalan ya gabatar saboda shigar ranar sallah karama.

Labrai bai bayyana adadin mutanen da aka yiwa afwan a ko wani bangare ba.

3613297


captcha