Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin timesofoman cewa, dukkanin wadannan mutane da suka muslunta sun fito ne daga kasashen Uganda, Philipines Sri Lanka da kuma India.
Babban dalilin musluntarsu dai na da alaka ne da samun amsoshin da suke bukata a cikin addinin muslunci dangane da rayuwa da kuma da kuma sahihiyar akida ta addini, kuma mafi yawa daga cikinsu mata ne.
Jobli Aleto wata ‘yar kasar Philipines ce da take zaune a kasar Oman, ta bayyana cewa tun kimanin shekaru biyu da suka gabata ne ta zo kasar, to amma akwai abubuwan da dama da ske damunta arayuwarta shi ne rashin natsuwa a cikin ranta dangane da akida ta addini, to amma a cikin wanann shekaru biyu ta karanta kur’ani kuma ta samu natsuwa da abin da ke ciki, wanda hakan ya sa ta muslnta.
Ta kara da cewa, daga lokacin da ta musulunta ta dukkanin kuncin da ke cikin ranta na rashin natsuwa ya kau baki daya.