IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Na Wakafin Musulunci A Sudan

23:01 - July 12, 2017
Lambar Labari: 3481694
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron kara wa juna sani na wakafin muslunci a kasar Sudan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ina cewa, taron da aka gudanar ya samu halartar wasu daga cikin masana da malamai na kasar ta Sudan da kuma wasu daga kasashen ketare.

Sumayya Muhammad Ahmad Abu Kashwa daya daga cikin wadanda suka jagoranci shirya gudanar da wanann zaman taro ta bayyana cewa, wannan taro yana da matukar muhimamnci ta fuskoki da dama.

Ta ce daga cikin muhimman abubuwan da suke tattare da wannan taro, akwai karfafa juna dangane da lamarin addini da kuma bayani a kan halin da duniyar musulmi take ciki gami da irin gudunmawa da musulmi za su iya bayarwa gwargadon ikonsu.

Bayan nan kuma akwai batutuwa na ilmantar da al’umma wadanda ake tattaunawa kansu, wanda kowa zai iya bayyana mahangarsa akan abin da za a yi domin ci gaban musulmia duk inda suke.

Wannan taro shi n ekaro na biyar da ake gudanar da shi tare da halartar masana na cikin gida da kasashen waje, kuma an dauki tsawon kwanaki biyu ana gudanar da shi a babban birnin kasar ta Sudan.

3618332


captcha