Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labara na libyaobserver ya bayar da rahoton cewa, jami'an gwamnatin Libiya na cewa duk da cewa maharan sun yi barazanar kisa a kan ma'aikatan gidan radiyon, to ganin cewa sun yi awan gaba da kudaden gidan radion na Kimamil-andalos, hakan ya fayyace mafunarsu na cewa barayi ne.
Kasar Libiya ta fada cikin rikici ne tun bayan da kungiyar tsaro ta Nato ta kifar da gwamnatin marigayyi kanar Mu'amar Kaddafi a shekarar dubu biyu da sha daya.
Kasashen yammacin turai ne suka taka gagarumar rawa tare da yan ta’adda da ke samun goyon bayan wasu sarakunan larabawa wajen kifar da gwamnatin Libya tare da hargitsa kasar.