IQNA

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas

22:55 - July 31, 2017
Lambar Labari: 3481753
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Ali Asgar Musawiyan matashi dan kasar Iran mai fasahar rubutu ya bayar da kyautar kwafin kur'ani ga hubbaren Abbas (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Kafil cewa, Sayyid Ali Asgar Musawiyan mai fasahar rubutu daga kasar ya bayar da wannan kwafin kur'ani da ya rubuta da hannunsa ga hubbaren Abul Fadl Abbas (AS).

Ya ce hakika yana farin ciki alfahari da wannan aiki, yana mai fatan aikin nasa ya karbu, ya kara da cewa yana niyar gudanar da wani aiki makamancin wannan domin bayarwa kyauta ga sauran wurare masu tsarki da ke Iraki.

Wannan kwafin kur'ani na daga cikin kur'anai guda 9 masu kima matuka, idan aka yi la'akari da salon da aka yi amfani da shi wajen rubutunsa.

Marubucin ya ce ya kwashe shekaru biyu yana yin aikin rubtun, kuma a kowace rana ya kan yi kamar sa'oi goma akan aikin wannan kwafin kur'ani mai tsarki, amma cikin ikon Allah ya samu ya kammala aikinsa, ya kara da cewa ya yi amfani da tawada ta musamman da masana harkar rubutu suka hada domin gudanar da wanann aiki.

A nasu bangaren masu kula da hubbaren Abbas (AS) ya jinjina wa wanann matashi, dangane da irin kokarin da ya yi wajen gudanar da wannan aiki mai abarka.

A lokacin maulidin Imam Ali (AS) ma Ali Asgar Musawiyan ya mika wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka ruuta akan shafuka masu ruwan zinariya ga hubbaren Imam Ali (AS).

3624984


An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas

An Bayar Da Kyautar Kur'ani Ga Hubbaren Abbas
captcha