IQNA

Masoyan Imami Na Takwas Daga Iyalan Gidan Manzo / Masu Hidimar Radawi A Afirka

23:52 - August 02, 2017
Lambar Labari: 3481759
Bangaren kasa da kasa, masoyan iyalan gidan manzon Allah sun halarci taron tunawa da zagayowar lokacin haihiwar Imam Ridha (AS) A Tanzania.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masoya iyalan gidan amnzon Allah sun halarci ofishin jakadan jamhuriyar Isalama kasar Tanzania.

Wannan tawaga dai ta hada malamai da masana da suka taru domin tunawa da zagayowar wannan lokaci mai albarka da ake tunawa da haihuwar limami na takwas (AS) daga limaman shirin masu tsarki na iyalan gidan manzon Allah.

Taron ya gudana a masallacin Alghadir inda aka gabatar da jawabai dangane da rayuwar wannan limami mai tsarki ga mahalrta wurin, da suka hada da baki ‘yan kasashen waje da kuma masu hidima a hubbarensa mai tsarki.

An gudanar da taron bayan kammala sallar Maghrib da kuma Isha, inda daya daga cikin masu hidima a hubbaren nasa ya yi bayani.

Ali Bagheri shugaban ofishin kula da al’adun muslunci na Iran a kasar Tanzania ya gabatar da nasa jawabin dangane da matsayin Imam Ridha (AS) da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen isar da sakon addinin Allah.

Hakimin Nishabour daya ne daga cikin malamn Ahlu sunnah, ya kasance yana cewa, a duk lokacin da na fuskanci wata matsala na kan tafi hubbaren Imam Ridha (AS) in yi addu’a, kuma bukata tana biya da ikon Allah.

Hojjatol Islam Khosroupanah daya daga cikin malaman da suka halrci ya gabatar da nasa jawabin dangane da matsayin Imam Ridha (AS) da kuma irin hadisan ilimi da aka karbo daga gare shi.

Daga karshe an girmama masu hidima a hubbaren Radhawi da suka halarci wurin wannan taro.

3625938


captcha