IQNA

Kammala Aikin Gyaran Wani Kur’ani Na Tarihi A Masar

23:52 - August 08, 2017
Lambar Labari: 3481777
Bangaren kasa da kasa, an kammala aikin gyaran wani kwafin kur’ani mai tsarki na tarihi a kasar Masar bayan kwashe tsawon shekaru shida ana aikin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar alwatan cewa, Ahmad Shauki shugaban cibiyar Darul Kitab babbar cibiyar kasar Masar da ke kula da ayyukan adana kayan tarihi da suka danganci rubuce-rubuce ya bayyana cewa, an kawo karshen wannan aiki da cibiyarsa ta gudanar.

Ya ci gaba da cewa wannan kwafin kur’ani mai tsarki an rubuta shi ne tun lokacin Khalifa Usman, daga cikin kr’anan da yasa aka rubuta domin aikewa da su zuwa biranna muslnci.

Al-shauki ya kara da cewa, kwarrau kan aikin gyaran takardu da rubutu na tarhi ne suka gudanar da wannan gagarumin aiki na tsawon shekaru shida a jere, domin gyara wannan kwafin kur’ani wanda ya samu matsala sakamakon jimawa da kuma ajiya ta dogon zamani.

Tun shekaru 100 da suka gabata ne dai aka dauko wannan kur’ani daga masallacin Amru bin As zuwa cibiyar Darul Kitab domin adana shi da kuma kula da shi.

Yanzu haka dai bayan kammala wannan aiki, za a fito da wannan kwafin kur’ani domin nuna shi ga mutane, musamman masu zuwa kasar domin ganin abbuwan tarihi da kasar take da su.

3627592


captcha