IQNA

An Kawo Karshen Horo Kan Kur’ani A Senegal

23:54 - August 08, 2017
Lambar Labari: 3481778
Bangaren kasaa da kasa, an kawo karshen wani shiri na horo kan kur’ani a kasar Senegal na malaman kur’ani a birnin mabiya darikar muridiyyah.

Kamfanin dillancin labaran uqnha ya bayar da rahoton cewa, bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci ya bayyana cewa, an an kammala wannan shiri na bayar da horo ne ga malaman kur’ani a makarantar Darul Manar da ke garin Tuba babbar cibiyar mabiya darikar muridiyya, tare da halartar fitaccen makarancin kur’ani na kasar Iraki Zakilu da ma wasu malamai.

Wannan dais hi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannans hiri akarkashin ofishin kula da al’adun muslcni na Iran da ke kasar ta Senegal, wanda ya samu halartar Sayyid Hassan Ismati, shugaban ofishin.

Shirin na bayar da horo kan hukunce-hukuncen karatun kur’ani da kuma yadda ake rera shi da salon a tangimi, ya samu halartar malamai 30 daga larduna 14 na kasar ta Senegal, wadanda suka kwashe tsawon kwanaki uku a jere suna samun wannan horo.

Daga karshe kuma an ba su kyautuka na kwafin kur’ani mai tsarki da aka buga ajamhuriyar muslucni ta Iran.

3628235


captcha