IQNA

Horo Ga Dalibai Musulmi Kiristoci Da Musulmi A Zimbabwe

22:10 - August 13, 2017
Lambar Labari: 3481793
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani shiri na bayar da horo ga dalibai musulmi da kiristoci a kasar Zimbawe.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci ta jamhuriyar muslunci ta Iran cewa, an gudanar da wannan shiri a cikin nasara akasar Zimbabwe.

Bayanin ya ce shugaban ofishin yada al'adun muslunci a kasar ta Zimbabwe Mohsen Shuja Khani da kuma mataimakin ministan ilimi na kasar, gami da Hojjatol Islam Ali Mahdi malami daga cibiyar ilimi ta Qomm su ne suka jagoranci rufe taron.

Wannan taro dai ya samu halartar daliban jami'a 50 da suka hada da musulmi da kiristoci, babbar manufar hakan ita ce kara samar da yanayi na hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai na kasar, musamman ma mabiya addinin kirista da ba su da masaniya akan muslunci da koyarwarsa.

Daga cikin abubuwan da aka bayar da horon akansu har da mahangar muslunci a kan zamantakewa da kuma kyawan dabi'u da tasirinsu a cikin dukkanin bangarori na rayuwar al'umma.

Wannan dai yan adga cikin ayyukan da cibiyar yada al'adun muslunci ta jamhuriyar muslunci take gudanarwa akasashe dban-daban na nahiyar Afirka, da nufin samar da yanayi na kyakywar fahimta a tsakanin mabiya addinai daban-daban da kuma msuulmi, tare da fahimtar da su cewa addinin muslunci addinin zaman lafiya da kaunar juna.

3629859


پایان دوره آموزشی «اسلام و مسیحیت» در زیمبابوه + عکس


captcha