IQNA

Ana Zargin Kungiyar Neo-Nazi Da Shirin Kai wa Musulmi Hari A Birtaniya

23:51 - August 14, 2017
Lambar Labari: 3481798
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Birtaniya sun fara farautar wasu mutane 40 Mambobi a kungiyar Neo-Nazi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Sportingcewa, jami’an tsaron kasar Birtaniya sun sanar da cewa sun shiga farautar wasu mutane masu matukar hadari, wadanda dukkaninsu mambobi na klungiyar masu tsatsauran ra’ayin kin jinin baki, da ake kira da Neo-Nazi.

Bayanin ya ce jami’an tsaron sun shiga farautar mutanen ne bayan samun bayanai da ke nuni da cewa, kungiyar na shirin kaddamar da wasu hare-hare a kan masallatai da kuma wasu cibiyoyin musulmi a cikin kasar ta Birtaniya.

Ana zargin kungiyar ta Neo-Nazi da hannu a kisan gillar da aka yi wa ‘yar majalisar dokokin kasar Birtaniya Jo Cox, wadda ta kasance a sahun gaba wajen kare hakkokin musulmin kasar ta Birtaniya, kamar yadda kuma a kowane lokaci take nuna goyon bayanta ga al’ummar Palastinu.

An kashe Jo Cox ‘yar majalisar dokokin Birtaniya a karkashin inuwar jam’iyyar Labour a cikin shekara ta 2016da ta gabata, inda kungiyar ta Neo-Nazi ta fito ta bayyana farin ciki da kuma goyon bayan hakan, lamarin da yasa jami’an tsaron zargin ‘ya’yan kungiyar a kan wannan lamari.

Al’ummar kasar Birtaniya dai suna kallon wannan kungiya a matsayin kungiyar ta’addanci wadda ba ta da bambanci da Daesh da sauran kungiyoyin masu dauke da irin akidarta.

3630162


captcha