Wadannan malamai biyu sun yi tafiya zuwa kasar Burkina Faso ne domin gudanar da wani shiri na karatun kur'ani mai tsarki, da kuma ganawa da malamai addinin musluncia kasar, inda suka rasa rayukansu a jiya a lokacin musayar wuta da 'yan bindiga da suka yi garkuwa da jama'a a wani wurin cin abinci na Turkawa a birnin Wagadugu tun a daren Lahadin da ta gabata.
Sarkin Kuwait Sabah Jabir Ahmad sabah ya aike da jirgi na musamman domin dauko gawwakin mutanen biyu da nufin dawo da su gida domin yi musu janaza a cikin iyalansu.
Babbar jami'a mai kula da siyasar wajen tarayyar turai Federica Mogherini ta yi Allah wadai da kakakusar murya dangane da harin na Burkina Faso, tare da bayyana hakan a matsayin aiki na dabbanci.
Mutane 18 ne dai suka rasa rayukansu sakamakon harin, da suka hada da 'yan kasar ta Burkina faso da kuma wasu 'yan kasashen ketare.