Malaman addinin muslunci da kuma masana kan halayyar dan adam ne suke jagorantar shiri, tare da saka ajujuwa na koyarwa da kuam wayar da kai a kan hakikanin koyarwar muslunci kan muhimamncin zaman lafiya da kaunar juna da kuma taimakekeniya a tsakanin al'umma.
Masana halayyar dan adam da ke cikin shirin suna ganawa da iyalan wadanda hare-haren Boko Haram suka rutsa da su, domin kwantar musu da hankali da kuma basu shawarwari, musamman ma wadanda lamarin ya cutar da lafiyarsu ko hankalinsu.
Najeriya ta ce za ta fadada wannan shirin tare da sauran makwabtanta da suke fama da irin wannan matsala ta hare-haren Boko Harama cikin kasashensu.