IQNA

Watan Agusta Watan Girmama Musulmi A Amurka

21:26 - August 15, 2017
Lambar Labari: 3481801
Bangaren kasa da kasa, wasu mazauna jahar California a kasar Amurka sun gudanar da bukuwan ayyana watan Agusta amatsayin watan girmama musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, a shekarar da ta gabata ce Bill Quirk dan siyasa akasar Amurka daga jahar California ya mika wani daftarin kudiri ga majalisar jahar domin nemana amince da watan Agusta a matsayin watan girmama musulmin Amurka.

Wannan daftarin kudiri ya samu karbuwa daga 'yan majalisar jahar California, wadanda suka amince da wannan daftrain kudiri, inda daga wanann shekara watan Agusta yana a matsayin watan da za a rika girmama musulmi a kowace shekara a cikinsa a jahar.

Ana sa ran wannan shirin zai ci gaba da yaduwa a cikin kasar ta Amurka, wanda zai kara bayar da damar samun fahimtar juna tsakanin msuulmi da sauran mabiya addinai na kasar ta fuskokin rayuwa da kuma zaman lafiya da juna.

Mu'inah Shaik ita ce ta kafa wani kamfe mai taken haduwa da musulmi a cikin jahar ta California, ta bayyana abin da wannan dan siyasa ya yi da cewa, hakika ya nuna wa duniya cewa a kasar Amurka akwai mutane masu lamiri masu sanin ya kamata, ba duka aka taru aka zama day aba.

3630576


captcha