IQNA

Fadada Bincike Kan Muslunci Tsakanin Iran Da Zimbabwe

23:22 - August 16, 2017
Lambar Labari: 3481802
Bangaren kasa da kasa, malama Cilindio Jengovanise daya ce daga cikin malaman da suke koyar da addinai musamman muslunci a jami’ar Zimbabwe.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a ci gaba da kara karfafa alaka ta fuskar bincike a dukaknin bangarori na ilimi tsakanin Iran da Zimbabwe, malamar jami’a Cilindio Jengovanise daga kasar ta Zimbabwe ta iso kasar Iran.

Babbar manufar zuwan nata dais hi ne, samar da yanayi na bincike a kan ilmomi na addinai tsakanin kasashen biyu, inda za ta gudanar da wani aikin bincike kan muslunci da tarihinsa a kasar Iran, da kuma irin rubuce-rubuce da malamai suka yi a fagage daban-daban na ilimi.

Daga cikin muhimamna bubwan da take dubawa wadanda malamai suka yi rubutu a aknsu, har da bangaren ilmomi na zamantakewa a mahangar muslunci, da kuma sauran bangarori da manyan malamai suka bayar da gundunmawa akansu, kamar likitanci da kuma lissafi da ilmomin taurari.

Kasashen Iran da Zimbabwe dai suna da kyakyawar laka a dukkanin bangarori na siyasa da kuma harkokin tatalin arziki da al’adu, kamar yadda kuma bangaren bunkasa harkokin ilimi ayake a kan gaba a cikin abubuwan da suka hada kasashen biyu.

3631271


captcha