IQNA

Fitaccen Mai Daukar Hoton Aikin Hajji ya Rasu

21:51 - August 17, 2017
Lambar Labari: 3481805
Bangaren kasa da kasa, Abdulaziz Al-furaikha fitaccen mai daukar hoton aikin hajji dan kasar Tunisia ya rasu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na radiosabrafm ya bayar da rahoton cewa, Abdulaziz Al-furaikha ya rasu ne sakamkon bugun zuciya a ranar Talata da ta gabata.

A lokacin rayuwarsa dai ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yada hotunan da yake dauka a lokutan aikin ahjji, wadanda suka yi tasiri matuka tun shekaru fiye da hamsin da suka gabata.

Ya rubuta wani littafi mai suna hajji zuwa dakin Allah mai alfarma, wanda aka tarjama shi a cikin harsuna daban-daban, kuma aka yada shi a kasashen duniya domin amfanin masu karatu.

Wannan mutum ya yi suna a duniya wajen kwarewarsa a bangaren aikinsa na daukar hoto, duk kuwa da cewa yana bayar da muhimamnci ne ga abubuwa da suka shafi addinin muslunci da tarihin muslunci a cikin aikin nasa.

Al-furaikha an haife shi ne a cikin shekara ta 1941 1 garin Safaqis na kasar Tunisia, kuma a nan ya tashi tun daga lokacin rayuwarsa ta kuruciya.

3631556


captcha