IQNA

Qatar Ta Ce Bai Kamata A Saka Siyasa Cikin Batun Hajji Ba

23:53 - August 18, 2017
Lambar Labari: 3481809
Bangaren kasa da kasa, a wani abu da ake kallonsa a matsayin sassauci a rikici diflomatsiya na tsakanin kasahen Qatar da Saudiyya, sarki Salman ya bada umurnin bude iyakar kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Imarat yau ya habarta cewa, matakin yazo ne domin baiwa mahajjatan kasar ta Qatar ne damar shiga kasar domin gudanar da aikin hajjin bana.

Babu dai wani abu da yake nuna cewa ko matakin na da nasaba da warware rikicindiflomatsiyya na tsakanin kasashen biyu, amman tuni masu sharhi suka bayyana cewa hakan wata alama da Saudiyya ke son nuna cewa bata sakasiyasa a cikin harkokin aikin hajji.

A kwanan baya dai an yi ta zargin Saudiyya da sanya siyasa a cikin harkokin shirya aikin hajji.

A daya bangaren wani babban jami’i a masarautar Qatar ya ce bai kamata a sanya batun siyasa a cikin batun aikin hajji ba, wanda dukkanin musulmi suke da hakkin gudanar da shi.

3631700


captcha