IQNA

Bikin Kammala Gyaran Kwafin Kur'ani Mafi Jimawa A Masar

23:21 - August 19, 2017
Lambar Labari: 3481811
Bangaren kasa da kasa, a gobe ne za a gudanar da bikin kammala gyaran kwafin kur'ani mai tsarki mafi jimawa a kasar Masar, wanda zai gudana a garin Kistata na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar yanar gizo na Yaum Sabi cewa, a gobe za a gudanar da bikin kammala gyaran kwafin kur'ani mai tsarki mafi jimawa a kasar Masar wanda aka gudanar a karkashin cibiyar adana kayan tarihi karkashin kulawar Ahmad Shauki shugaban cibiyar.

Wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin Masar da suka hada da ministoci da kuma fitattun malamai da manyan 'yan siyasa da masana za su halarci wurin taron wanda za a gudanar a gobe Lahadi.

Daga cikin wadanda za su halarci taron har da ministan kula da ayyukan al'adu na kasar Hilmi Al-namnam, sai kuma babban mai bayar da fatawa na kasar baki daya Shauki Allam, sai kuma tsohon mai bayar da fatawa Ali Juma'a, sai kuma tsohon ministan al'adun Shaker Abdulhamid.

Baya ga haka kuma a bangaren cibiyoyin addini akwai wakilai daga babbar cibiyar addini ta kasar wato Azhar, sai kuma wasu cibiyoyi na kur'ani da suka turo nasu wakilan daga sassa daban-daban na kasar Masar wadanda duk za su halarci tarona gobe.

Ana danganta wannan kwafin kur'ani da lokacin mulkin Khalifa Usaman dan Affan wato khalifa na uku, inda ake bayyana cewa yana daga cikin kur'anan da ya bayar da umarni a rubuta a birane na musluncia wancan lokacin, amma dai ana gudanar da bincike domin tabbatar da hakan.

Aikin gyaran kur'anin dai ya dauki tsawon shekaru shida ana gudanar da shi, inda wasu kwararru ta fuskar irin wanann aiki suka gudanar da shi.

3631826


captcha