IQNA

Taron Bayar Da Horo Kan Sanin Muslunci A Zimbabwe

23:24 - August 19, 2017
Lambar Labari: 3481812
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron bayar da horo kan samun masaniya dangane da addinin muslunci wanda cibiyar muslunci ta Qom ta shirya a birnin Harare na Zimbabwe.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun musulunci cewa, an gudanar da wannan shiri a cikin nasara.

Daga cikin abubuwan da aka gudanar a wurin taron dai har da koyar da wasu daga cikin muhimamn darussa da suka shafi akidar muslucni, inda aka yi bayani a kan wani littafi da ke yin magana a kan hakan da aka rubuta a cikin harshen turanci wato Islamic belief system.

Malam Ali Mokhtarian shi ne ya jagoranci wannan shirin, wanda aka aike da shi musamman daga cibiyar yada addinin muslunci ta birnin Qom domin jagorantar wanann shiri na bayar da horo a kasar ta Zimbabwe, sai kuma sai kuma Mohsen shojaei Khani shugaban ofishin yada al'adun muslunci na Iran akasar.

Taron yana daga cikinsa wadanda aka gudanra ashekaru baya, inda wananns hi ne karo na uku da ake gudanar da shi a wanann kasa ta Zimbabwe wadda akasarin mutaneta mabiya addinin kirista ne, duk kuwa da cewa dai ba su da wata matsala da msuulmi.

Babbar manufar shirin dai ita ce kara karfafa musulmi da bayanai na ilimi a kan muslunci da kuma akidarsa, da kuma yin zaman lafiya da sauran al'ummomi da ba msuulmi ba, da kuma nuna musu kyawawan dabiu da musulunci yake koyarwa.

3632158


captcha