IQNA

Koyar da Matasan Senegal Ilimin Ahlu Bait (AS)

22:24 - August 21, 2017
Lambar Labari: 3481818
Bangaren kasa da kasa, ofishin kula da harkokin al'adun muslunci na jamhuriyar muslunci ta Iran akasar Senegal ya shirya wani horo kan ilimin ahlul bait (AS) a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kula da al'adun muslunci cewa, an shirya gudanar da wanann horo ne ga matasa 80 'yan kasar Senegal, wanda aka fara a jiya.

Sayyid Hassan Esmati shi ne shugaban ofishin, ya kuma gabatar da jawabi a lokacin bude taron bayar da horon, inda za a koyar da su ilmomin ahlul bait (AS) da kuma matsayinsu a cikin adinin muslunci.

A cikin bayanin nasa ya bayyana cewa, sun yi la'akari da yanayin hutun bazara ne da ake gudanarwa a wanann lokaci, wanda kuma za su yi amfani da wannan damar domin isar da sakon ahlul bait (AS) ga matasan wannan kasa ta msuulmi masu matukar son iyalan gidan manzon Allah.

Horon dai zai dauki tsawon kwanki 21 ana gudanar da shi, tare da hadin gwiwa da jami'ar Almustafa (SAW) a reshenta na kasar ta Senegal.

3632764


captcha