IQNA

23:06 - September 26, 2017
Lambar Labari: 3481937
Bangaren kasa da kasa, tashar radion kur’ani ta kasar Masar tana shirin fara aiwatar da wani shiri na saka wasu daga cikin tilawar kur’ani na tsoffin makaranta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Hasan Salman shugaban gidan radion kur’ani na kasar Masar ya sanar da cewa, tashar tana shirin fara aiwatar da wani shiri na musamman inda za ta rika saka wasu daga cikin tilawar kur’ani na tsoffin makaranta na kasar.

Manufar shirin dai ita ce raya tsoffin kira’oin da aka yi, wadanda a halin yanzu ba a cika samunsu cikin sauki ba, wanda sauraren su zai taimaka masu karatu matuka wajen samun salon a kira’a ta fitattun makaranta.

Abin tuni a nan dai shi ne, wanna radio shi ne na farko a kasar masar, kuma shi ne irinsa na farko a kasashen msulmi da aka bude tun shekaru fiye da sattin da suka gabata, domin gabatar da karatun ur’ani da dukkanin abin da ya shafi kur’ani mai tsarki.

3646540


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: