IQNA

13:51 - September 28, 2017
Lambar Labari: 3481942
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da guanar da tarukan makokin Ashura a kasar Tanzani a an gudanar da zama a masallacin Ghadir da ke birnin Darussalam.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyr yada ala'adun muslucni cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Tanzania ya dauki nauyin shirya taruka na Ashura.

A cikin faifan bidiyo da aka dauka na wannan zaman makoki, Nazzar Qatari ne yake gabatar wakokin makokin Ashura, a cikin harsunan larabci da kuma farisanci.

Wannan mutum dai asalinsa dan kasar Iran ne amma yana zaune a kasar Qatar, wanda hakan yasa yake gabatar da wakokinsa na Ashura acikin harsunan farisanci da kuma larabci.

Wani abin burgewa shi ne yadda wani karamin yaro ya hardace abin da yake fada a cikin harsuna biyu, kuma a nan take ya mayar da shi a cikin harshen sawahili da ake Magana da shi a yankin.

3647416


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Ashura ، Tanzania ، Nazzar Qatari ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: