IQNA

13:55 - September 28, 2017
Lambar Labari: 3481944
Bangaren kasa da kasa, Masu binciken sun sanar da cewa mai yiyuwa ne a yau alhamis su shiga yankin Musulmi Rakhin da ke kasar Myanmar domin ganin halin da musulmi suke ciki daga kusa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A yau alhamis ne ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke gabacin Asiya, ya fitar da sanarwa da ta kunshi cewa a karon farko masu bincike na majalisar sun sami izinin gwamnatin kasar Myanmar domin shiga kasar da kuma isa yankin Rakhine na tsirarun musulmin kasar.

Gwamnatin kasar ta Myanmar ta bada izinin shiga yankin na Musulmi ne adaidai lokacin da kwamitin tsaron Majalsiar Dinkin Duniya ya yi zama na musamman akan lamarin.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniyaya ce masu binciken za su shiga cikin kasar ta Mayanmar bisa aiki tare da gwamnatin kasar.

Har ila yau ya ce; Shugabannin hukumomi daban-daban da su ke karkashin Majalisar Dinkin Duniyar za su kasance a tare da masu binciken.

3647566


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: