IQNA

Taron Dararen Ashura A Cikin Watan Muharram A Birnin Hague

21:07 - September 29, 2017
Lambar Labari: 3481946
Bangaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da tarukan raya daren ashura a cikin wannan wata na Muharram a brnin Hague na kasar Holland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na alcauther.com ya bayar da rahoton cewa, cibiyar alkauthar tana ci gaba da shirya taruka a cikin dararen goma na farkon Muharram, domin tunawa da abubuwan da suka faru da Imam Hussain (AS) a cikin irin wannan lokaci.

Daga cikin muhimamn abubuwan da ake gudanarwa a babban ginin wannan cibiya, har da gabatar da bayanai kan hakikanin ashura da kuma abubuwan da suka faru a cikinta, gami da fitar da darussa da musulmi za su dauka daga wannan babbar waki’a.

Daga cikin masu gabatar da jawabi akwai Sayyid Ridha Hussaini da kuma Haj Ja’afar Badri, da Jalil Ahmad Khairpour, wadanda dukkaninsu suna gabatar da bayanai kan hakikanin abin da ya faru a cikin wadannan darare ga Imam Hussain (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah da suke tare da shi.

Cibiyar darul kur’an da ke Hollanda karkashin cibiyar alkauthar tana daukar nauyin shirya tarukan addini da ska hada da tarukan ashura, wanda ke samun halartar musulmi mazauna brnin.

3647712


captcha