IQNA

16:52 - September 30, 2017
Lambar Labari: 3481948
Bangaren kasa da kasa, mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki suna cikin babbar tawagarsu a tsakanin masu makokin Ashura a tsakanin Haramain.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin dar-alquran.org cewa, mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki suna cikin babbar tawagarsu a tsakanin masu makokin Ashura a tsakanin hubbarori biyu masu tsarki.

Masu makokin dai suna dauke ne da tutoci da kuma kwafin kur'anai a hannuwasu da suke dagawa sama, a matsayin alama ta juyiyin Ashura da kuma nuna matsayin tawagarsu ta mahardata da makaranta kur'ani mai tsarki, domin kara daukaka matsayin kur'ani a cikin wannan taro mai albarka.

Wannan dai ba shi ne karon farko da makarantar kur'ani da mahardata suke shiga cikin tawagogi domin gudanar da tarukan tunawa da zagayowar Ashura ba.

Koa shekarun baya an gudanar kamar haka, inda tagawar takan kunshi malamai masu koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki, da kuma dalibai da suka hada da makaranta da kuma mahardata.

3647811


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: