IQNA

Sayyid Hassan Nasrullah:
23:40 - October 01, 2017
Lambar Labari: 3481955
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Hassan Nasrullah ya ce dole ne a dauki matai kan masu daukar nauyin ta’addanci da kuma kawo akrshen hijirar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa za su debi kashinsu a hannun matukar gigi ya debe su suka kaddamar da yaki a kan kungiyar Hizbullah yana mai kiran yahudawan da suka yiyo hijira zuwa "Isra'ila" da su gaggauta komawa inda suka fito.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin ranar Ashura a birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon a yau din nan inda yayin da yake magana kan barazanar da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu yake yi na kaddamar da yaki a kan kungiyar ta Hizbullah ya ce matukar gigi ya debe shi ya kaddamar da wannan yaki, to kuwa ba za su ji ta dadi ba.

Sayyid Nasrallah ya kirayi yahudawan da suka yiyo hijira zuwa "Isra'ilan" da cewa Netanyahu da maso goya masa baya musamman shugaban Amurka na yanzu Donald Trump suna amfani da su ne kawai, don kuwa matukar dai yaki ya barke to su ne za su zamanto makashi kana zakaran gwajin dafi.

Yayin da ya koma kan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh kuwa, Sayyid Nasrallah ya ce wajibi ne a ci gaba da yakarsu har sai an ga bayansu yana mai jaddada wajibcin hukumta wadanda suka kirkiro kungiyar da kuma ba ta goyon baya na kudi da makamai yana mai ishara da irin rawar da Saudiyya ta taka a wannan bangaren.

3647953


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: