IQNA

23:18 - October 02, 2017
Lambar Labari: 3481957
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman karshe na makokin shahadar Imam Hussain (AS) wanda ya zo daidai da lokacin shahadar Imam Sajjad (AS) a husainiyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagora.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na jagora cewa, a yau an gudanar da zaman karshe na makokin shahadar Imam Hussain (AS) wanda ya zo daidai da lokacin shahadar Imam Sajjad (AS) a husainiyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagoran juyin juya halin musulunci.

A wurin taron Hojjatol Islam Husaini Qomi ya gabtar da jawabi, inda ya tabo muhimman lamurra da suka shafi rayuwar Imam Sajjd (AS) a bangarori na ilimi da da siyasa da kuma hikimar da ya yi amfani da ita wurin jagoranci,a lokacin da azzaluman sarakuna na bani Umayya suke da dukkanin madafun iko na yankunan musulmi.

Wannan limamin shiriya ya shinfida hanyar da sauran limamai da suka biyo bayansa suka hau wajen shiryar da al’ummar musulmi zuwa ga sahihin tafarki na manzon Allah bisa koyarwar ahlul bait amincin Allah ya tabbata a gare su, musamamn limaman da suka biyo bayansa kai tsaye, wato Imam Baqir (AS) da kuma Imam Sadeq (AS).

Bayan an kuma Morteza Taheri da kuma Saeed Haddadiyan sun gudanar da wakokin makoki.

3648459


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: