IQNA

23:29 - October 02, 2017
Lambar Labari: 3481960
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani taron baje kolin tarjamar kur'ani mai tsarki a yankin Newham na kasar Birtaniya.
Baje Kolin tarjamar Kur'ani A LondonKamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na newham recorder ya bayar da rahoton cewa, an fara baje kolin ne tare da gabatar da littafan kur'ani mai tsarki da aka tarjama acikin ahrsuna guda 50 a wurin.

Bayanin ya ci gaba da cewa, kur'anan da aka tarjama a cikin harsuna daban-daban na duniya ana yin amfani da su ne a kasashen da ake yin Magana da wadannan harsuna domin amfanin musulmi.

Busharat Ahmad daya daga cikin wadanda suka shirya wannan baje koli ya bayyana cewa, wannan yana daga cikin manyan tarukan baje koli da ak agudanar a kasar.

Ya kara da cewa, babbar manufar baje kolin it ace yada zaman lafiya a tsakanin al'ummomi kamar yadda kur'ni yake yin kira, wanda hakan ne ya sanya ake baje kurnai da ak atarjama a cikin harsuna daban-daban domin ganina bin da wannan littafi yake fada.

Baje kolin yana samun halartar mutane daban daban da suka hada da musulmi da wadanda ba musulmi ba, inda sukan duba kurnai da kuma yin yin tambayoyi kana bin da ya shige musu duhu.

3648207 نمایشگاه ترجمه‌های قرآن کریم در لندن

 نمایشگاه ترجمه‌های قرآن کریم در لندن

 نمایشگاه ترجمه‌های قرآن کریم در لندن


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: