IQNA

23:32 - October 02, 2017
Lambar Labari: 3481961
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatocin Bangladesh da Myammar sun cimma yarjejeniyar kafa wani kwamiti na aiki tare da nufin dawo da daruruwan 'yan gudun hijira musulmin Rohingya gida bayan sun gudu daga kisan kiyashin da sojoji da 'yan Buddha suke musu a jihar Rakhine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an cimma yarjejeniyar ce a yau din nan Litinin tsakanin ministan harkokin wajen BangladeshAbul Hassan Mahmood da wani babban jami'in gwamnatin Myammar din Kyaw Tint Swe a birnin Dhaka, babban birnin kasar Bangladesh din.

Ministan harkokin wajen Bangladesh din ya shaida wa manema labarai cewa gwamnatin Myammar din ta amince ta bari 'yan gudun hijiran su dawo gida, don haka bangarori biyu za su kafa kwamitin aiki tare don cimma wannan manufar.

Tsawon makonnin da suka gabata din kimanin musulmin Rohingya 510,000 ne suka gudu daga kasar zuwa Bangladesh sakamakon kisan kiyashin da sojojin gwamnati da mabiya addinin Buddha masu tsaurin ra'ayi suke musu.

3648319


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Myanmar ، Bangaladesh ، Rohingya ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: