IQNA

16:56 - October 03, 2017
Lambar Labari: 3481962
Banaren kasa da kasa, an jinjina wa jagoran kiristoci mabiya darikar Kalotila paparoma kan matsayar da ya dauka kan batun kisan kiyashin da ake yi wa msuulmi a kasar Myanmar inda aka mika lambar yabo kan haka ga wakilinsa a kasar Ghana Gabriel Palmar Bakleh.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, bangaren yada labarai na cibiyar yada aladun muslucni ya bayar da bayanin cewa, a jiya Muhammad hassan Ipikchi karamin jakadan Iran a Ghana ya jinjina wa jagoran mabiya darikar Kalotila paparoma kan matsayar da ya dauka kan batun kisan kiyashin da ake yi wa msuulmi a kasar Myanmar inda aka mika lambar yabo kan haka ga wakilinsa a kasar Ghana Gabriel Palmar Bakleh wanda zai aike masa da shi.

Irin matakin da jagoran kiristoci mabiya darikar katolika ya dauka, a akan batun matsalar kisan kiyashin da ake yi musulmi a kasar Myanmar abin yabawa da jinjinawa, domin kuwa ya tabbatarwa duniya cewa shi mutum na kowa mai kishin dukkanin 'yan adam ba sai kiristoci ba.

Karamin jakadan an Iran ya ce hakika doniya tana bukatar mutane irin su paparoma Francis, domin kuwa a halin yanzu babban abin da ake bukata shi ne zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin dukkanin al'ummomin, kuma ba za ta samu sai an samu jagororin addini masu fahimta da ilimi da kuma son zaman lafiya da karfafa shi a tsakanin al'ummomin duniya, kamar yadda paparoma yake yi.

Kasar Ghana na daga cikin kasashen nahiyar Afirka masu yawan ambiya addinin kirista duk kuwa da cewa akwai musulmi amsu yawa a kasar, amma dukkanin bangarorin suna zaune lafiya da juna.

3648718


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: