IQNA

23:34 - October 03, 2017
Lambar Labari: 3481963
Bangaren kasa da kasa, kauyen shaikhiya da ke cikin lardin Qena a kudancin kasar Masar na daga cikin yankuna da ake buga misali da su wajen lamarin kur’ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na Bawwabah News ya habarta cewa, kauyen shaikhiya da ke cikin lardin Qena a kudancin kasar Masar na daga cikin yankuna da ke taka gagarumar rawa wajen lamarin kur’ani a kasar ta Masar.

Wannan kauye dai yana da mutanen kimanin dubu 12 da suke rayuwa a cikinsa, haka nan kuma a cikinsa ana samar da fitattun makaranta da kuma mahardata, sakamakon irin tarbiya da suka samu tun kakanninsu masu riko da kur’ani ma tsarki.

Baya ga haka kuma akwai manyan dakunan karatu na addini da suka kunshi nauoin bugu na kur’ani, da kuma littafan addini masu tarin yawa da suka hada da tafsirai.

Haka nan kuma akwai masalatai da suke da bangarori na koyarwa musamman inda ake koyar da karatun kur’ani ga dalibai da kuma kananan yara.

Abdulfattah Ali Muraze daya ne daga cikin datijai na wannan kauye, ya bayyana cewa sun tashin sun iyayensu da kakanninsu suna mayar da hankali matuka ga lamarin kur’ani, wanda hakan ya sanya tarbiyar dukkanin al’ummar wannn kauye ta ginu ne akan riko da kur’ani.

3648630


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Qena ، kasar Masar ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: