IQNA

16:35 - October 04, 2017
Lambar Labari: 3481966
Bangaren kasa da kasa, mata mahardata kur'ani mai tsarki ya zuwa yanzu aka tabbatar da cewa za su halarci gasar kur'ani ta hadaddaiyar daular larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na MENAFN ya bayar da rahoton cewa, a cikin shekaru kimanin ashirin da daya daga cuka gabata ne aka fara gudanar da gasar kur'ani ta duniya ta Dubai.

Kafin wannan lokaci ana gudanar da gasa amma ba a matsayi na kasa da kasa ba, inda daga bisani aka fara gayyatar makaranta da mahardata daga kasashen duniya, kuma a halin yanzu wannan gasar ta birnin Dubai ita ce gasar kur'ani mafi daukar hankali a duk kasashen larabawa.

Abdulrahim Hussain Ahli shi ne shugaban kwamitin gudaarwa na wannan gasa, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun aike da goron gayyata ga kasashe 140, da suka hada da na musulmi da kuma wadanda ban a musulmi ba, inda ya zuwa yanzu wakilan kasashe 64 aka tabbatar da zuwansu, kuma ana ci gaba da jiran sauran kasashen.

Zahra Sadat Hussaini yar shekaru 10 da haihuwa wadda ta hardace dukaknin kur'ani mai tsarki ita ce za ta wakilci Iran a gasar.

A shekarar Bara Hananah Khalfi ce ta wakilci Iran a wannan gasa.

3649264


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: