IQNA

16:37 - October 04, 2017
Lambar Labari: 3481967
Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin kwamandojojin kungiyar Hizbullah ya yi shahada a ci gaba da tsarkake yankunan Syria da ake yi daga 'yan ta'addan wahabiyawan takfiriyyah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na tashar almanar ya bayar da rahoton cewa, Ali Alhadi Ashiq daya daga cikin kwamandojojin Hizbullah ya yi shahada a musayar wuta da 'yan ta'adda a yankin Tadmur na Syria a ranar Litinin da ta gabata.

Bayanin ya ce za a gudanar da janazar wannan kwamanda a yau a garin Ala'in da ke cikin gundumar Ba'albak a kasar Lebanon.

Shahid Abdulhadi ya kasance daya daga cikin manyan kwamandojin Hizbullah da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen fatattakar 'yan ta'addan wahabiya takfiriyya daga yankunan Qusair na Syria acikin shekara ta 2013, sai kuma Qalamu a 2014, da kuma Ersal a cikin wannan shekara ta 2017.

3649059


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: