IQNA

23:23 - October 05, 2017
Lambar Labari: 3481969
Bangaren kasa da kasa, Ahmad said wani matashi dan kasar Masar mai shekaru 14 ya nuna fatansa na ganin ya rubuta kur’ani mai tsarki da hannunsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alwatan ya habarta cewa, Ahmad said a halin yanzu dalibin makarantar sakandare ne, kuma ya fito ne daga yankin Mansura.

Ahmad yana da fatan ganin ya rubuta kur’ani mai tsarki a cikin shekara ta 2020, indsa a halin yanzu yakan yi amfani da lokacin da yake samu ne kawai na karshen mako domin rubuta abin da ya sawaka, lamarin da ya sanya aikin nasa baya yin sauri.

Wannan matashi dai yana da kyawun rubutu, wanda hakan ne ya sanya shi ya sdauki alkawalin cewa zai yi amfani da wannan baiwa da Allah ya bashi domin rubuta kur’ani mai tsarki baki daya domin godiya ga Allah madaukakin sarki.

Mahaifin Ahmad ya saka shia kan hanyar rubutun kur’ani mai tsarki tun yana dan shekaru 10da haihuwa, ganin cewa yanayin rubutunsa ‘yan mutane kalilan ne suk da baiwa irinta.

Haka nan kuma Ahmad ya bayyana cewa yana burin ganin ya yi karatu a bangaren injiniya, domin yi ma kasarsa hidima, inda a halin yanzu yake mayar da hankali ga bangarorin da yake son ya samu kwarewa a kansu.

3649391


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: