IQNA

23:25 - October 05, 2017
Lambar Labari: 3481970
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin kiristanci da muslunci sun gudanar da zama a babbar majami’ar Winchester a kasar Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai Christian Daily cewa, an gudanar da wannan zaman taro ne tare da halartar wakilan musulmi da kuma na kiristoci a wannan majami’a.

Babbar manufar taron dai ita ce kara samun fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, da kuma yin Allah wadai da ayyukan da wasu suke aikatawa na cin zarafi ga musulmi sakamakon ayyukan ta’addanci da wasu suke aikatawa a da sunan muslunci.

Dukkanin bangarorin biyu sun yi Allah wadai da ayyukan ta’addanci daga kowane bangare suka fito, tare da jaddada cewa musulunci da kiristanci ba addinai na ta’addaci ba, addinai ne na zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummomi.

3649461


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، addinai ، musulmi ، bangare ، Birtaniya ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: