IQNA

Ayatollah Sayyid Ahmad Khatami:
23:56 - October 06, 2017
Lambar Labari: 3481971
Bangaren siyasa, Ayatullah Ahmad Khatami waanda yake magana akan matsayar Amurka danagne da yarjejeniyar Nukiliyar, ya ce; Babu wani abu da ya saura da Amurkan ba ta take ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin na Tehran ya ci gaba da cewa; A lokuta da dama jami'an gwamnatin Iran sun sha bayyana cewa; Babu fagen sake kulla wata sabuwar yarjejeniyar ta Nukiliya, wanda hakan shi ne daidai.

Har ila yau, limamin juma'ar ya yi ishara da yadda kasashen Turai suke goyon bayan ci gaba da aiki da yarjejeniyar, sannan ya kara da cewa; Idan har turawan za su fuskanci zabi tsakanin mu'amala da Iran ko Amurka za su zabi Amurka ne.

A cikin kwanakin bayan nan, Amurka tana yin magana akan yarjejeniyar Nukiliyar Iran tare da kokarin sauya ta, ko yin watsi da ita.

Tun kafin wannan lokacin dai Iran ta bayyana matsayinta na kin amincewa da rarraba kasar Irakim tare da bayyana hakan a matsayin wani sabon makirci na Amurka da Isra’ila da shirin tarwatsa kasashen larabawa.

Haramtacciyar kasar Isra’ila ce dai a halin yanzu kawai ta amince da batun kafa kasar Kurdawa aarewacin kasar Iraki lamarin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga kasashen duniya.

3649627


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: