IQNA

23:57 - October 06, 2017
Lambar Labari: 3481972
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya sun kai samame a masallacin aqsa mai alfarma a daidai lokacin fara idin yahudawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar yada labarai ta Palastinawa ta bayar da rahoton cewa, yahudawa 83 da ke samun kariya daga jami’an tsaron haramtacciyar gwamnatin yahudawa.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da yahudawan suke fara gudanar da idinsu da ske gudanarwa a kowace shekara, inda suke keta alfarmar masallacin aqsa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan bas hi ne karon farko da yahudawa suke keta alfarmar masallacin aqsa ba, domin kuwa a shekarar bara a bin suka yi kenan, kamar yadda kuma suka keta alfarmar wasu wuraren na msuulmi da suka hada da masallatai da makabartu na annabawa.

Al’ummar Palastinawa suna cin zaman rashin tabbatas a wannan birni ganin irin matakan da yahudawan suke dauka awannan karo wanda ga alama suna da nufin rubanya cin zarafin jama’a fiye da sauran lokuta.

3649312


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: