Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan gasa wadda aka fara gudanar a matsayi na kasa da kasa, a shekarar da ta gabata, za ta ci gaba da gudana akaro na biyua wannan mataki.
Gwamnan lardin Adil Gadban ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu an kammala dukkanins hirye-shiryen da suka kamata domin aiwatar da wannan shiri, inda yanzu haka ana cikin gudanar da wata gasar ta share fage.
An dauki tsawon shekaru goma sha hudu ana gudanar da wannan gasa amma a matsayi na cikin gida kawai a yankin na Port said, inda mahardata daga dukkanin bangarori na kasar Masar suke halartar gasar.
Amma a halin yanzu wannan gasa ta tashi daga matsayin gasar hardar kur'ani ta cikin gida ta koma gasa ta duniya, inda mahardata daga kasashen duniya suke halarta kamar yadda aka yi a shekarar da ta gabata, kuma a bana ma da yardarm Allah za a gudanar.