IQNA

Fitaccen Marubucin Kur'ani Dan Masar Ya Rasu

22:12 - October 09, 2017
Lambar Labari: 3481982
Bangaren kasa da kasa, Mahmud Ibrahim Salama fitaccen marubucin kur'ani mai tsarki dan kasar masar ya rasu yana da shekaru 98 da haihuwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto shafin yada labarai na egynews.net cewa, Mahmud Ibrahim Salama ya rasu bayan hidima ta shekaru da dama a bangaren kur'ani mai tsarki.

Mahmud Ibrahim Salama an haife shi ne a cikin shekara ta 1919 a kauyen Muslimiyya a cikin gundumar Zaqaziq a kasar Masar.

Ya rubuta kur'ani a cikin salo daban-daban har sau hudu, da suka hada da kur'ani mai fadi da tson 35x50CM, sai kuma wani mai fadi da tawo 70x100CM.

Allah ya karbi rayuwarsa a daren Juma'a da ta gabata, inda mutuwarsa ta daga hankulan al'ummomin kasar Masar, kasantuwarsa mutum ne da ya yi suna wajen yin hidima ga kur'ani da kuma son yada koyarwar wannan littafi mai tsarki.

Hilmi Namnam ministan kula da harkokin al'adu na kasar Masar, ya fitar da sakon ta'aziyya dangane da rasuwar wannan mutum, tare da bayyana rashinsa amatsayin babban rashi ga al'ummar Masar da ma musulmi baki daya.

3650895



Fitaccen Marubucin Kur'ani Dan Masar Ya Rasu

Fitaccen Marubucin Kur'ani Dan Masar Ya Rasu

Fitaccen Marubucin Kur'ani Dan Masar Ya Rasu

Fitaccen Marubucin Kur'ani Dan Masar Ya Rasu
captcha