Baya ga batun Palastinu, an tabo batutuwa da suka halin da musulmi suke cikia kasashen Syria, Myanmar, Yemen da Afghanistan, da kuma tunanin samo hanyoyin taimaka masu da fitar da su daga halin da suke ciki.
Abdulrahman Iskandar shi ne shugaban masallacin quds na kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, wannan taro yan ada matukar muhimamnci dangane da samun hanyoyin taimaka ma musulmi da suke fuskantar matsaloli.
Babbar manufar taron dai ita ce tattauna batun Palastine, a gefen haka kuma na tattauna sauran batutuwa na kasashen msuulmi, taron ya samu haartar masana 400 daga sassa na kasar da wasu kasashe.