IQNA

Ministan Palastinu Ya Kirayi Palastinawa Da Su Kasance A cikin Masalalcin Aqsa

16:50 - October 11, 2017
Lambar Labari: 3481989
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Yusuf Ad'is minista mai kula da harkokin addini a Palastine ya kirayi al'ummar musulmi mazauna birnin quds da su kasancea cikin masallacin aqsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, a cikin 'yan kwanakin nan yahudawan sahyuniya suna ci gaba da keta alfarmar masllacin aqsa mai alfarma.

Baya ga wanann birni mai alfarma, ko a ranar Litin da Talatar da suka gabata daruruwan yahudawan sahyuniya ya share wuri zauna sun kai samame a kan masallacin alkhalil, da sunan raya idin yahudawa.

A wata zanatawa da ya yi yau da tashar talabijin ta Palastine Sheikh Yusuf Ad'is ya bayyana cewa, ganin abin da yahudawan suke ya fara wuce gona da iri, ya zama wajibi a nasu bangaren Palastinawa su zama cikin shirin kare wuraren masu tsarki.

Ya bayyana cewa masalalcin aqsa yana a matsayin jan layi da ba a tsallake shi, a kan haka musulmi su ci gaba da kasancewa a wannan masalalci a kowane lokaci domin kare alfarmar daga keta alfarmarsa da yahudawa ke yi.

Haka nan kuma ministan na Palastinu ya bukaci sauran bangarori na kasa da kasa da su sauke nauyin da ya rataya akansu wajen ganin sun kare hakkokin musulmi da yahudawan sahyuniya suke ketawa.

3651739


captcha