IQNA

Tattaunawar Musulmi Da Cocin Katolika A New York

16:52 - October 11, 2017
Lambar Labari: 3481990
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman tattaunawa da aka saba gudanrwa na shekara-shekara sakanin musumi da cocin katolika a birnin new York.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na silive cewa, an gudanar da zaman ne wajen wani cin abincin dare da aka shirya, tare da halartar malamai daga bangaren addinin muslunci da kuma shugabannin majami'ar.

Brayen Mike Winey shi ne babban malami na cocin katolika ta birnin New York ya bayyana a wajen taron cewa, tun kimanin shekaru 15 da suka gabata ne suka fara gudanar da irin wannan zama tare da 'yan uwansu musulmi da nufi kara karfafa alaka da fahimtar juna.

Na'in Bik shi ne babban daraktan cibiyar bunkasa harkokin muslunci a arewacin Amurka ya bayyana a wajen taron cewa, hakika irin wannan haduwa tana da matukar muhimmanci, domin kuwa tana kara tabbatar da wajabcin zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin kiristanci da muslunci wadanda 'yan uwan juna.

3651658


captcha