IQNA

Gasar Kur’ani A Tsakanin Jami’oi 5 Na Kasar Pakistan

23:35 - October 19, 2017
Lambar Labari: 3482014
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da al’adun muslunci ta kasar Iran ta shirya wa jami’oi biyar da ke kasar Pakistan gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar kula da al’adun muslunci ta kasar Iran ta shirya wa jami’oi biyar da ke kasar Pakistan gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki wanda za a gudanar gobe Litinin a dakin taruka na Khaibar da ke jami’ar muslunci a Bishawur.

Bayanin ya ce daga cikin jami’oin da za su halarci wannan gasa akwai jami’ar karatun bangarorin injiniya, sai kuma jami’ar koyon aikin likitan hakora, da kuma jami’ar jami’ar muslunci.

Taron dai zai samu halartar wasu daga cikin malaman jami’oin da kuma wakilan dalibai gami da wasu daga cikin jami’a gwamnatin kasar ta Pakistan, kamar yadda jami’ai daga kasar Iran za su halarci taron gasar.

Bayan kammala wannan gasa, cibiyar kula da harkokin al’adun muslunci ta kasar Iran za ta bayar da kyautuka ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.

3654387


captcha