IQNA

Masu kyamar Musulmi Na Hankoron Hana Gina Masallaci A Sweden

23:35 - October 20, 2017
Lambar Labari: 3482019
Bangaren kasa da kasa, gungun wasu masu adawa da addinin musulunci a kasar Sweden sun kaddamar da wani kamfe domin ganin sun kawo cikas ga wani shirin gina masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Risalehaber cewa, tun a lokutan baya aka fara ikin ginin wai masalaci a garin Halmestad na kasar Sweden, amma masu tsananin adawa da addinin muslunci suna ta kwo cikas ga aikin.

Yanzu haka irin wadannan kungiyoyin sun fara kadamar da wani kamfe domin tunzura saran mutane yankin da suki amincewa da wannan shiri, kamar yadda uma suke ta kai gwauro su kai mari a wurin mahukuntan kasar.

Wannan masallaci dai kamar sauran masallatai da musulmi suka gina a kasar, an bi ta hanyoyi na doka da kuma kiyaye dukkanin kaidoji, saboda haka bab wani abu da musulmi suka yi wanda ya sabawa doka wajen ginin masallacin, kamar yadda bangaren shari’a na kasar ya tabbatar.

Wasu daga cikin wadannan mutane masu kyamar muslunci a kasar ta weden sun aike da sakonni ta hanyoyin kafar sadarwa da adiresin cibiyar musulmi cewa, za su dauki matai rusa wannan masallaci ko da an gina tare da izinin hukuma.

3654612


captcha