IQNA

Musulmi Mata Na Scotland Sun Tattara Taimako Ga Musulmin Rohingya

23:33 - October 22, 2017
Lambar Labari: 3482028
Bangaren kasa da kasa, musulmi mata na kasar Scotland sun tattara taimako domin aikewa ga musulmin Rohinguya da e gdun hijira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani shiri na taimakon musulmi, wasu daga cikin musulmi mata na kasar Scotland sun tattara taimako domin aikewa ga musulmin Rohinguya da e gdun hijira bayan korarsu daga kasarsu.

Bayanin ya ci gaba da cewa ana tattara wannan taimako n daga dukkanin bangarori na musulmi mata, inda suke bayar da taimako na kayan sakawa wato tufafi da kuma barguna gami da kayan abinci da kudade.

Wannan yana daga cikin abin da wasu daga cikin msuulmi sukeyi a wasu kasashe domin taimakon yan uwansu da ae yi wa kisan kiyashi Myanmar da uma aka kora dubbandaruruwa daga cikinzuwa gudun hijira tare da kone gidajensu da kadarorinsu da kuma kashe su.

Tun kafin wannan lokacin dai was ‘yan kalilan daga cikin kasashen msuimin sun aike da taimako kuma suna ci gaba da aikewa da shi domin ganin wadannan bayin Allah sun samu sauki, kasar da ke kan gaba wajen wannan aiki ita ce Iran sai kuma wasu kasashen nahiyar asiya.

3655427


captcha