IQNA

Zaman Farko Na Masoya Ahlul Bait (AS) Da Fada Da Kungiyoyin Takfiriyya

23:55 - November 22, 2017
Lambar Labari: 3482128
Bangaren kasa da kasa, A safiyar yau ne aka bude wani taron kasa kasa kan fada da kungiyoyin ta'addanci na takfiriyya a nan birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran taron da ya sami halartar manyan malamai da masana daga kasashe da dama na duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan taro na kwanaki biyu da aka bude shi a safiyar yau Laraba ya sami halartar sama da malamai 500 na Shi'a da Sunna daga kasashe 90 na duniya sannan kuma manufarsa ita ce tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen fada da wannan annoba ta ta'addanci da tsaurin ra'ayin addini wanda shi ne tushen hakan.

Taron dai an bude shi ne da jawabin babban mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin kasashen waje kana kuma shugaban majalisar farkawa ta Musulunci Dakta Ali Akbar Wilayati wanda a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewar makira al'ummar musulmi suna ta kokari ne wajen haifar da rarrabuwan kai da rashin tsaro a kasashen musulmi da nufin cimma bakaken aniyar da suke da su ciki kuwa har da wawashe dukiyoyin kasashen musulmin.

A yayin zaman na yau dai wani adadi na mahalarta taron sun gabatar da jawabansu da kuma mahangarsu kan wannan batu

A gobe Alhamis ne dai ake sa ran za a kawo karshen taron da kuma fitar da sanarwar bayan taro bayan tattaunawa da kwamitocin da aka kafa za su yi da nufi gano hanyoyin da za a cimma wannan manufa ta fada da ta'addancin.

3665904


captcha