IQNA

An Bude Taron Makon Hadin Kai Karo Na 31

15:47 - December 05, 2017
Lambar Labari: 3482170
Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka bude babban taron makon hadin al'ummar musulmi mai taken hadin kai da ci gaban musulmi tare da halartar shugaban jamhuriyar muslunci Hojjatol Islam Dr Hassan Hassan Rauhani.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, 'yan mintunan da suka gabata ne aka bude babban taron makon hadin kan al'ummar msuulmi a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran tare da malamai da masana da masana a babban dakin taruka na birnin.

Wannan taro wanda shi ne karo na talatin da daya da ake gudanar da shi, yana samun halartar baki kimanin 500 daga sassa na duniya, da nufin kara karfafa hadin kan al'ummar musulmi da kuma tabbatar da cewa musulmi sun zama cikin fadaka a kan halin da aka jefa su a ciki.

An kafa kwamitoci guda 6 wadanda za su gudanar da zama tare da tabbatar da cewa an bi diddigin dukkanin abubuwan da aka cimmawa, daga cikin kwamitocin akwi kwamitin hadin kan musulmi da kuma ci gaban al'ummar musulmi a zaman yau, haka nan kuma akwai kwamitin bunkasa al'adun musulunci da rarrabewa tsakaninsu da al'adun yammacin turai, sai kuma kwamitin ayyukan alkhairi, haka nan kuma za a kafa wasu kwamitocin na daban da suka shafi gwagwarmayar malaman musulunci.

3669615

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha