IQNA

Trump Ya Amince Da Birnin Quds A Matsayin Fadar Mulkin Isra’ila

23:49 - December 06, 2017
Lambar Labari: 3482174
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar Amurka ya yi furuci da kasancewar birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Trump Ya Amince Da Birnin Quds A Matsayin Fadar Mulkin Isra’ilaKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A jawabin da ya gabatar dazu-dazun nan a yau Laraba: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi furuci da Qudus a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila duk da kiraye-kirayen da duniya ta masa kan ya nisanci wannan furuci saboda ya yi hannun riga da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Har ila yau shugaban na Amurka ya kuma bada umurni ga ma'aikatar harkokin wajen kasar kan ta fara gudanar da shirye-shiryen mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qudus daga Tel-Aviv.

A cikin jawabinsa Donald Trump ya bayyana cewa: Dukkanin siyasar shugabannin Amurka da suka gabata na kin yin furuci da Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, siyasa ce da bata yi nasara ba, don haka wannan mataki da ya dauki shi ne siyasar da ta dace kuma wadda zata haifar da zaman lafiya a cewarsa.

3670361

 

 

 

 

 

 

captcha